Home Labarai Dole ne sai Oshiomhole ya yi murabus – Matasan APC

Dole ne sai Oshiomhole ya yi murabus – Matasan APC

72
0

A ranar Litinin din nan ne wasu gungun masu zanga-zanga suka dirarwa shelkwatar APC da ke Abuja suna neman shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole ya yi murabus kana bun da suka kira rashin iya tafiyar da mulki.

Da suke magana da ‘yan jarida masu zanga-zangar na kungiyar matasan APC masu ruwa da tsaki, karkashin jagorancin Agricola Ejembi sun koka da yadda ake samun kwan-gaba-kwan-baya tun lokacin da Oshiomhole ya karbi jagorancin jam’iyyar.

Masu zanga-zangar sun nuna yadda jam’iyyar ke samun koma baya musamman a jihohi da suka ce yanzu haka jam’iyyar ta kare ne da gwamnoni 18 zuwa 17 daga cikin 24 da take da su a baya.

A don haka suka bukaci shugaban jam’iyyar ya gaggauta yin murabus ko jam’iyyar ta samu damar farfadowa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply