Ganin abun da ya biyo bayan zanga zangar EndSARS, gwamnatin tarayya ta ce akwai buƙatar sake gina aminci tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka.
Mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya bayyana haka lokacin taron ƙaddamar da gidauniyar sake gina Lagos, wanda ya gudana a Ikeja.
Osinbajo ya ce akwai buƙatar gwamnatoci a dukkan matakai su sake dawo ƙwarin guiwa da yarda a tsakanin su da mutane, don kaucewa sake faruwar ɓarnata kayan da aka yi a ƙasar, silar zanga-zangar EndSARS.
