Home Labarai D’Tigers ta lallasa takwararta ta Mali

D’Tigers ta lallasa takwararta ta Mali

76
0

Kungiyar kwallon kwando ta Nijeriya D’Tigers ta tsallake zagayen farko na gasar kofin zakarun Afrika na shekarar 2021.

D’Tigers ta lallasa takwararta ta Mali da ci 91-68 a yayin zagayen wasan a kasar Rwanda.

Tunda farin wasan, ‘yan wasan kasar ta Mali ne suke gaba, kafin daga baya ‘yan wasan na D’Tigers na Nijeriya suka fara casa su.

Ya zuwa yanzu ana dakon fitar da hadin wasan na gaba da za a yi cikin watan Febrairun 2021, a inda Nijeriya ke jagorantar rukuni na 4 na D.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply