DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeKetareDubban 'yan Nijar sun fito zanga-zangar goyon bayan shugaba Tchiani bayan dakile...

Dubban ‘yan Nijar sun fito zanga-zangar goyon bayan shugaba Tchiani bayan dakile masu bore a kasar

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, a birnin Yamai ranar Laraba, bayan da sojojin da ke biyayya ga gwamnatin suka dakile wani yunkurin bore a karshen makon da ya gabata.

Rahotanni sun ce zanga-zangar ta tattaro dubban ‘yan Nijar, ciki har da magoya bayan gwamnatin sojin da wasu ministoci, a dandalin Place de la Concertation. Haka kuma, an shirya gudanar da makamantan zanga-zangar a wasu manyan biranen kasar.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito boren ya haifar da kazamin fada a wasu muhimman wurare a Yamai, kafin dakarun da ke biyayya ga gwamnatin su samu nasarar shawo kansa tare da taimakon mayakan haya na Rasha daga rundunar Africa Corps.

Tun bayan yunkurin boren, Janar Tiani, wanda ya karbi mulki a juyin mulkin shekarar 2023, bai fito bainar jama’a ko yin wani jawabi ba.

A yayin zanga-zangar, an rika daga tutocin Rasha tare da rera taken nuna adawa da kasashen yammacin duniya. Ministan kasuwanci, Abdoulaye Seydou, ya ce al’ummar Nijar za su nuna wa duniya cewa suna da hadin kai, kuma cin amana ba za ta karya musu guiwa ba.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Tiani, Janar Amadou Ibro, ya zargi wasu da daukar nauyin boren daga kasashen waje. Gwamnatin sojin ta kuma taba zargin Faransa, tsohuwar kasar da ta yi wa Nijar mulkin mallaka, da hannu a yunkurin boren, duk da cewa ba a gabatar da hujjar jama’a da ta tabbatar da zargin ba.

Kasashen Nijar, tare da Mali da Burkina Faso, sun kara kusantar Rasha tun bayan juyin mulkin, yayin da kasashen uku suka yanke alaka da Faransa tare da neman hadin gwiwar Moscow wajen yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi da ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Sahel.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata