Home Labarai Duk dan bindigar da ya kawo AK47 za a bashi shanu 2...

Duk dan bindigar da ya kawo AK47 za a bashi shanu 2 a Zamfara

118
0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, yace gwamnatinsa za ta ba shanu 2 ga duk bindiga samfurin AK 47 da dan bindiga ya kawo wa gwamnatin jihar.

Gwamna Matawalle na magane a lokacin da ya karbi bakuncin babban sufeton ‘yansanda na Nijeriya Muhammad Adamu da sauran shugabannin tsaro na kasa.

Gwamnan yace jihar ta sha fama da harin ‘yan bindiga, ya kara da cewa idan jami’an tsaro za su yi wa batun kofar-raggo, to kuwa za a kitse shi cikin kankanin lokaci.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply