Gwamnatin tarayya ta umarci manyan shugabannin asibitocin kasar da su bude rajistar masu zuwa aiki kan, likitocin kasar.
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bada wannan umarni bayan wata ganawa da shugabannin kungiyar likitocin ya zo karshe a ranar Talata ba tare da cimma matsaya ba.
Ehanire ya umarci shugabannin asibitocin da su bude rajistar ne daga ranar Larabar nan da misalin karfe 7 na safe, don tantance wadanda suka zo aiki da wadanda ba su zo ba.
Ya ce duk wadanda ba su zo aikin ba, za a kaddara masu sun ajiye aikin su ne.
A ranar Litinin ne dai kungiyar likitocin ta Nijeriya suka shiga yajin aiki bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da suka ba gwamnatin tarayya.
Saidai shugaban kungiyar Aliyu Sokomba, ya ce likitocin za su janye yajin aikin ne kadai a cikin sa’o’i 24 idan har gwamnatin tarayya ta zo da kwakkwaran tayi na biya masu bukatun su.
