Home Sabon Labari Duk ma’aikacin bogin da ya ke son gamawa lafiya ya dawo da...

Duk ma’aikacin bogin da ya ke son gamawa lafiya ya dawo da albashin da ya karba, za mu yi masa afuwa- Gwamnan Ebonyi

71
0

 Saleem Ashir Mahuta

 

Gwamnatin jihar Ebonyi ta fito da wani tsarin sasanci tsakaninta da ma’aikatan bogi da aka kama a yayin tantance ma’aikatan da aka gudanar a jihar. Gwamnatin jihar  ta ce dukkanin wanda ya amshi sulhun ba zai fuskanci shari’a ba

 

Sai  dai gwamnatin ta ja kunnensu ta na mai cewa dukkanin wanda ya ki amsar sabon tsarin da gwamnatin ta fito da shi zai fuskanci hukunci  kuma gwamnati za ta gano dukkanin kudaden da ya amsa a matsayin albashi daga aljihunta.

 

Bayanin hakan na kunshe  ne a cikin wata takarda da sakataren watsa labarai na Gwamna Emmanuel Uzor ya fitar a ranar Asabar. Takardar ta bayyana cewar tsarin sasancin zai kasance a tsakanin 30 ga watan Agusta zuwa 10 ga watan Satumbar da muke ciki. Ana kuma sa-ran ma’aikatan bogin za su gabatar da kansu ga hukuma a  wannan lokaci.

Tambarin gwamnatin jihar Ebonyi da ke Kudu Maso Gabashin Nijeriya

Takardar ta bukaci dukkanin wani ma’aikacin bogi da ya mika wuya tare da bin hanyoyin da aka tsara wajen mayar da kudaden da ya amsa ba bisa ka’ida ba.

 

Kazalika, takardar ta yi nuni da cewa  gwamnatin jihar  na farin ciki musamman ganin yadda aka samu ci gaba a yayin tantancewar wanda ya sa gwamnatin Jihar da ta kananan hukumomi ta samu rarar Naira miliyan 60 a kowanne wata.

 

Kuma gwamnatin ta bayyana cewar za ta ci gaba da zakulo dukkanin ma’aikatan bogin da ke amsar albashi ba bisa ka’ida ba  har sai an tabbatar an samu wasu damarmakin aiki ga sauran matasa marasa aikinyi.

 

 

 

 

 

Punch:       Saleem/Jani

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply