Home Kasashen Ketare Dumi-Dumi:Chelsea ta kori manajanta Lampard

Dumi-Dumi:Chelsea ta kori manajanta Lampard

32
0

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana korar kocinta Frank Lampard a ranar Litinin bayan zarginshi da kasa yin abin kwarai a gasar Firimiya.

Shugaban kulob din na Chelsea Roman Abramovich ya bayyana cewa “duk da kasancewar hukuncin, abu ne mai tsauri a kungiyar, sakamakon alakar da ke tsakanina da Lampard sannan ina matukar ganin girmanshi” Inji shi.

Kungiyar dai ta Chelsea ita ce ta 9 a kan teburin gasar ta Firimiya, da tazarar maki 11 tsakaninta da kungiyar Manchester United da ke jan ragamar teburin.

Lagon kungiyar dai ta Chelsea ya karye inda ta sha kashi a wasa 5 da ta buga cikin 8 bayan ta fara da karfinta.

Tsohon shugaban Paris Saint-Germain, Thomas Tuchel ne zai cigaba da jagorantar kungiyar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply