Home Labarai Edo: Babu Oshiomhole a jerin sunayen da Ize-Iyamu ya yi wa godiya

Edo: Babu Oshiomhole a jerin sunayen da Ize-Iyamu ya yi wa godiya

132
0

Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo da aka kammala kwanan nan Pastor Osagie Ize-Iyamu bai ambaci sunan Adams Oshiomhole ba a jerin sunayen wadanda suka ba da gudunmuwa a ya yin zaben.

Adams Oshiomhole dai ya ba da gudunmuwa sosai wajen komawar Ize-Iyamu APC daga PDP, kuma shi ne ummul-aba’isin ba shi titar takarar gwamna a jam’iyyar.

Ize-Iyamu ne dai ya zo na biyu a zaben, bayan da ya sha kaye daga hannun gwamna mai ci Mr Godwin Obaseki.

Daily Trust ta rawaito cewa Pastor Ize-Iyamu ya yi godiya ga shugaban kasa Muhammad Buhari da shugaban riko na APC na kasa Mai Mala Buni da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, da ilahirin gwamnonin APC.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply