Home Labarai EFCC ta gabatar da Maina a zaman kotu

EFCC ta gabatar da Maina a zaman kotu

97
0

Hukumar yaƙi da cin hanci ta Nijeriya EFCC ta gabatar da tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho Abdulrasheed Maina a gaban kotu yau Juma’a.

Maina wanda ke fuskantar shari’a kan zargin sama da faɗin Naira biliyan ₦2bn, ya tsallake belin da aka ba shi sannan ya gudu zuwa Nijar.

A ranar Alhamis ne kuma jami’an tsaro suka dawo da shi Nijeriya, mako biyu bayan kotu ta soke belinsa tare da umarnin a ci gaba da shari’ar tasa har zuwa lokacin da hukumomin tsaro za su gano shi.

An shigo da Maina cikin babbar Kotun Tarayyar da ke Abuja da misalin ƙarfe 8:27am na safiyar yau kafin daga bisani aka fara sauraron shari’ar da misalin ƙarfe 9am.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply