Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi EFCC ta gano bilyan 4.16 daga kamfanonin shirya gasanni “Lottery”

EFCC ta gano bilyan 4.16 daga kamfanonin shirya gasanni “Lottery”

115
0

Mukaddashin shugaban hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta Nijeriya Mohammed Abba ya ce hukumar ta gano kudi Naira bilyan 4.16 da kamfanonin shirya gasanni ba su biya ba.

Ya yi nuni da cewa wadannan kamfanonin ba su biyan haraji ga gwamnati, don haka ne EFCC ta saka baki.

Da ya ke jawabi ga kwamitin tabbatar da an biya harajin gwamnati, Mohammed Abba ya ce sun gano sama da Naira bilyan 4.16 daga kamfanonin shirya gasanni na Abuja, tare da gano sama da Naira bilyan 3 ga kamfanonin Legas.

A cikin wata takarda daga mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren, mukaddashin shugaban hukumar ya ba da tabbacin cewa za su shiga su fita don ganin an biya gwamnati hakkokinta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply