Home Labarai EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kwara

EFCC ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kwara

84
0

Hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC, ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kwara, Alhaji AbdulFatah Ahmed, don ya yi mata bayani a kan wasu matakai da ya zartas lokacin mulkinsa.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne da kansa a cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Ahmed ya ce “ A jiya, ina ofishin hukumar EFCC shiyyar Ilorin inda na amsa gayyatar da aka yi min.

“Babu wani zargin zamba da aka yi a kaina.

“Tuni kuma na koma gidana.” inji Ahmed

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply