DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeLabaraiEFCC ta janye ƙarar da ta shigar da matashiya Maryam Isah Shehu

EFCC ta janye ƙarar da ta shigar da matashiya Maryam Isah Shehu

Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa EFCC, Ola Olukoyede, ya umarci a janye karar da hukumar ta shigar kan Maryam Isah Shehu da Abubakar Shuraim Abdulhamad, wadanda aka gurfanar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja kan zargin aikata laifin yanar gizo da yada bayanan da ke bata wa hukumar suna.

An gurfanar da mutanen biyu ne a ranar Alhamis, 20 ga Agusta, 2026, a gaban mai shari’a Joyce Abdulmalik, bisa zargin cin zarafi ta kafafen sadarwa na yanar gizo (cyberstalking).

A cewar sanarwar da shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na EFCC, Dele Oyewale, ya fitar ranar Juma’a, hukumar ta ce abin da ake zargin wadanda ake karar sun aikata ya saba da sashe na 24(2) (c) na dokar laifukan yanar gizo ta 2015, wadda aka yi wa kwaskwarima a 2024.

Sai dai Olukoyede ya yi la’akari da rokon da mahaifin Maryam Shehu ya yi cikin tausayi, da kuma kiraye-kirayen wasu ‘yan Nijeriya na a janye karar, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Saboda haka, Oyewale ya ce shugaban EFCC ya umarci a janye karar da ake yi wa matasan biyu.

Sai dai hukumar ta gargadi jama’a cewa ba za ta lamunci kai wa martabarta hari da gangan ta kowace kafar sadarwa ba.

Hakan na nufin Maryam Shehu da Abubakar Shuraim ba za su ci gaba da fuskantar shari’a kan tuhume-tuhumen da suka kai ga gurfanar da su ba.

EFCC ta bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da hulda da ita cikin mutunci da bin ka’ida, tare da jaddada kudirinta na gudanar da ayyukanta bisa doka da kuma kare muradun kasa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata