Home Labarai EFCC ta janye tuhumar da take yi wa Mama Boko Haram

EFCC ta janye tuhumar da take yi wa Mama Boko Haram

15
0

Hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC shiyyar Maiduguri ta rufe karar da take yi a kan Aisha Alkali Wakil da aka fi sani da Mamar Boko Haram, a Babbar Kotun jihar Borno, karkashin jagorancin Alkali Umar Fadawu.

Masu shigar da karar sun rufe karar ne bayan gabatar da shaidunsu na karshe guda biyu da suka hada da Geoffrey Okolorie da Bashir Abubakar.

Alkali Fadawu y adage sauraron karar zuwa 1 ga watan Maris, 2021 domin ba wadanda ake kara damar kare kansu, tare da bada umurnin a ci gaba da tsare sauran wadanda ake zargin a gidan yarin Maiduguri

Wadda ake tuhumar ta farko Wakil, wadda ita ce shugabar wata gidauniyar bada agaji, ana tuhumarta ne tare da Prince Lawal Shoyade da Tahiru Saidu Daura bisa zargin sama da fadin Naira miliyan 40.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply