Home Labarai EFCC ta kama matasan da ke damfarar mutane ta intanet

EFCC ta kama matasan da ke damfarar mutane ta intanet

32
0

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta ce jami’anta sun yi nasarar cafke wasu matasa su 10 da ake zarginsu da damfara mai nasaba da kwamfuta da ake kira ‘Yahoo-Yahoo’.

Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar ta EFCC, ya ce an cafke wadanda ake zargin ne a makarantarsu ta ‘Academy’ da ke yankin Bwari na birnin Abuja inda aka ce su “su na koyon sana’ar yaudarar mutane ne”.

Wadanda ake zargin, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 30, su ne Sixtus Jude, Moses Samuel, Isalan Johnny, Dapet Nimshak, Samuel Ogboche, Victor Samuel, Victor Asuquo, Ibrahim Yunusa, Yahaya Usman da Chijoke Ikwuoha.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply