Home Labarai EFCC ta musanta zargin cin hanci kan Abdulrasheed Bawa

EFCC ta musanta zargin cin hanci kan Abdulrasheed Bawa

24
0

Hukumar yaki da cin hanci ta Nijeriya EFCC, ta karyata zargin cin hanci da wata jaridar intanet ta ce ana yi wa Abdulrasheed Bawa wanda ake kokarin tabbatarwa a matsayin shugaban hukumar.

A ranar Talatar makon nan ne, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar Dattawa ta tantance Bawa, domin nada shi shugaban hukumar.

Amma wata kafar yada labaran intanet ta buga wani labari da ke cewa a lokacin da Magu ke shugabantar EFCC an kama Bawa mai shekaru 40 kan zargin sayar da wasu tankunan mai 244 da aka kwace, a garin Fatakwal.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta bayyana zargin a matsayin marar makama, tana mai cewa babu hannun Bawa a sayar da tankunan man na Fatakwal.

Hukumar ta kara da cewa badakalar tankunan man na daga cikin dalilan da suka sa aka kori wasu daga cikin ma’aikatan na EFCC bayan bincike da kwamitin Alkali Ayo Salami ya yi.

Ta yi kira ga al’umma su yi watsi da wannan rahoto da ta ce ‘yan hana ruwa gudu ne suka dauki nauyinsa domin bata sunan shugaban hukumar ta EFCC na gobe.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply