Home Labarai EFCC za ta binciki manyan masu kuɗi na Kebbi

EFCC za ta binciki manyan masu kuɗi na Kebbi

203
0

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa, EFCC, za ta soma daukar kididdigar wasu mashahuran gidaje na wasu manyan Jami’an gwamnati a jihar Kebbi da ake zargin an same su ta haramtacciyar hanya.

Shugaban Hukumar mai kula da yankin Sokoto, Kebbi da Zamfara Alhaji Abdullahi Lawal, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da Gidan Radion Vision FM Birnin Kebbi.

Lawal ya ce da Zarar an kammala kididdiga da binciken wadannan haramtattun dukiyoyi ba za a yi wata-wata ba wajen gurfanar da wadanda suka mallake su a gaban kuliya.

Ya ce tun bayan kafa ofishin na Sokoto a shekarar 2019, hukumar ta samu nasarori da dama wajen kwato dukiyoyin da jama’a da aka yi sama da fadin su.

Ya kara da cewa Hukumar ta tilastawa ‘yan kwangila dake gina Babbar Sakatariyar jihar Kebbi, ci gaba da gini, bayan da aikin ya tsaya cak bayan gushewar Gwamnatin da ta gabata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply