Home Labarai El-Rufa’i ya bada umarnin cire rabin albashin ma’aikata don tallafa wa talakawa

El-Rufa’i ya bada umarnin cire rabin albashin ma’aikata don tallafa wa talakawa

142
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bada umarnin cire rabin albashin manyan masu muƙaman siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati domin samar da kuɗin bada tallafi ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar Lahadi ne gwamnatin jihar ta bada sanarwar tsawaita dokar hana fita a jihar zuwa kwanaki 30.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Muyiwa Adekeye ya fitar, ya ce waɗanda wannan umarni zai shafa sun haɗa da kwamishinoni, manyan sakatarori, masu bada shawara da shugabannin hukumomi.

A cewar sanarwar, El-Rufa’i ya bada umarnin cewa kowane daga cikin su, zai bada gudunmuwar Naira dubu ₦500,000 a cikin wannan watan na Afrilu, kafin daga bisani a riƙa cire rabin albashinsu na sauran watannin, har zuwa lokacin da komai zai daidaita.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply