Home Lafiya El-Rufa’i ya kamu da Covid-19

El-Rufa’i ya kamu da Covid-19

78
0

A daren ranar Asabar ɗin nan ne gwamnan jihar Kaduna ya sanar da cewa ya kamu da cutar coronavirus.

Malam Nasir El-Rufa’i ya ce a farkon satin nan ne aka ɗebi jinin sa, kuma da yammacin yau aka maido da sakamakon da ya nuna yana ɗauke da cutar.

“Kamar yadda ƙa’ida take yanzu haka na keɓance kai na don gudun yaɗa ta kamar yadda NCDC ta umarta.

“Ina so in yi kira ga jama’ar jihar Kaduna, su tabbatar suna bin ƙa’idojin kamuwa da cutar kamar yadda aka bayyana.

“Abu ne mai muhimmanci kowa ya bada gudunmuwar sa ta samun lafiya, ku zauna a gida don ku rayu.

“Mataimakiya ta ke jagorantar kwamitin yaki2da Covid-19 a jihar, kuma za ta ci gaba da fitar da bayanai lokaci zuwa lokaci.” In ji El-Rufa’i.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply