Home Labarai El-rufai ya yi alhinin rasuwar sarkin Zazzau

El-rufai ya yi alhinin rasuwar sarkin Zazzau

124
0

Gwamna Mal Nasiru Ahmad El-rufai na jihar Kaduna, ya yi jimamin rashin marigayi sarkin Zazzau mai martaba Alhaji Shehu Idris.

Gwamna El-rufai ya bayyana jimamin rashin a shafinsa na Facebook, ga ma abinda sanarwar ke cewa:

Cikin jimami: Ina cike da bakin ciki, tare da nuna alhini bisa rasuwar babban uban kasa a wannan jiha ta mu, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alh (Dr.) Shehu Idris CFR.

Ya rasu ne a wani asibitin sojoji da ke Kaduna a yau bayan gajeriyar rashin lafiya.

Haka an shirya za a yi masa sallar Janazah a Zariya da karfe 5 na yamma in Sha Allah.

Kuma za a bi duk ilahirin dokokin da hukumar kula da yaduwar cutuka ta tanadar ya yin janaizar don kaucewa bazuwar annobar Covid-19.

Tuni na sanar da Shugaba Muhammdu Buhari, GCFR game da wannan babban rashi, kuma na yi masa ta’aziyya.

Shugaban Ma’aikata na na fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ne zai jagoranci tawagar gwamnatin Tarayya zuwa Zariya don ta’aziyyar mai martaba don yiwa Majalisar Masarautar ta Zazzau da mutanen Masarautar Zazzau da Jihar Kaduna.

Mun yi rashin abin alfahari, tushen hikima da shiriya kuma uba na kwarai ga kowa.

Da fatan Allah ya jaddada rahma a gareshi.

Amin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply