Home Coronavirus Elrufai ya bude Kaduna gabadaya

Elrufai ya bude Kaduna gabadaya

185
0

Gwamnan Kaduna ya fitar da sanarwar cewa daga ranar Laraba ya sassauta dokar kulle da ya sanyawa jihar. Sai dai ya ce masu ratsa jihar da ababen hawa za su yi haka ne kawai a tsakanin karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma.

Gwamnan ya ce gwamnati ta yarda a bude gidajen abinci da otel otel da wasu sana’o’i . Sai dai dole kowa ya ci gaba da daukar matakan kariya.

To amma Gwamna Elrufai ya ce lokacin bude makarantu bai yi ba. Ya kuma yi gargadin cewa za a dawo da dokar corona indai nan da karshen watan nan aka samu karuwar masu corona a jihar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply