Home Labarai EndSARS: Gwamnatin Lagos za ta saki mutum 253 da aka kama

EndSARS: Gwamnatin Lagos za ta saki mutum 253 da aka kama

146
0

Kwamishinan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin jihar Lagos Moyosore Onigbanjo ya shawarci kotunan jihar su saki mutane 253 daga cikin waɗanda aka kama suna da alaƙa da zanga-zangar EndSARS.

Onigbanjo ya ce ɓangaren gabatar da ƙara na jihar, ya yi bitar tuhume-tuhumen da ƴan sanda suka gabatar kan mutanen, saidai sun kasa samun ƙwararan hujjoji kan laifukan da ake tuhumarsu da aikata wa.

Wata sanarwa da Daraktan harkokin yau da kullum na ma’aikatar shari’ar Kayode Oyekanmi ya fitar, ya ce Kwamishinan shari’ar ya yi bayanin cewa ƴan sanda sun gabatar masa da zarge-zarge 40 da ake yi wa mutum 361 da aka kama da alaƙar zanga-zangar ta EndSARS domin neman shawara, kuma a kan haka ne suka duba zarge-zargen tare da bada wannan shawara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply