Home Labarai EndSARS: Mutum biyu sun mutu an ƙona sama da motoci 50 a...

EndSARS: Mutum biyu sun mutu an ƙona sama da motoci 50 a Abuja

163
0

Aƙalla mutum biyu ake tsammanin sun mutu, sama da motoci 50 suka ƙone, bayan da wasu da ake zargin ƴan zanga-zangar EndSARS ne suka saka wa wani wurin gyaran motoci wuta a Apo, Abuja, ranar Litinin.

Wasu ne dai ake zargin sun shigo cikin zanga-zangar suka riƙa kai wa mutane hari tare da ƙone motoci.

Shaidun gani da ido sun ce ɓata garin sun zo ne cikin wata tirela tare da tarwatsa masu zanga-zangar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply