Home Labarai #EndSARS: SERAP ta yi tir da cin gidajen talabijin tara

#EndSARS: SERAP ta yi tir da cin gidajen talabijin tara

100
0

Kungiyar yaki da cin hanci ta SERAP ta yi tir da matakin cin tara da aka dauka kan tashoshin talabijin na AIT, Channels da Arise TV.

A ranar Litinin ne dai, Mukaddashin babban daraktan hukumar kula da kafafen radiyo da talabijin ta Nijeriya NBC Armstrong Idachaba ya ce tashoshin sun karya ka’idojin hukumar tare da ririta wutar rikici a Nijeriya ta hanyar dauko hotunan intanet su yada a tashoshinsu.

Saidai a sanarwar da mataimakin Daraktan SERAP Kolawole Oluwadare ya ce wannan mataki wani misali ne, na kokarin hukumomin Nijeriya wajen dakile ‘yancin cin gashin kan kafafen yada labarai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply