Home Addini Erdogan zai jagoranci bude Hagia Sophia da ta koma masallaci

Erdogan zai jagoranci bude Hagia Sophia da ta koma masallaci

153
0

Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyib Erdogan zai jagoranci bude masallaci a dadadden ginin nan na Hagia Sophia a yau Juma’a.

Ginin dai ya shafe shekaru 900 a matsayin coci ya koma masallaci tsawon shekaru 500 sannan ya yi shekaru 80 a matsayin gurin da aka kebe domin adana kayan tarihi.

Sai dai albarkacin gwagwarmayar da kungiyoyin Turkawa masu kishin addinin musulunci da su ka shafe tsawon shekaru su na yi da kuma burin shugaba Erdogan Hagia Sophia ta sake zama masallaci.

Sai dai tuni Fafaroma Francis ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da wannan hukunci da shugaba Erdogan ya yanke.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply