Home Wasanni Abin da ya sa Eto’o ya yi bankwana da tamaula

Abin da ya sa Eto’o ya yi bankwana da tamaula

63
0

Ahmadu Rabe

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da kuma Inter Milan, Samuel Eto’o ya sanar da cewa ya yi ritaya daga buga kwallo, bayan kwashe shekaru 22 yana taka leda a kungiyoyin kwallon kafa daban-daban.

Samuel Eto’o

Eto’o dan asalin kasar Kamaru mai shekara 38 ya fara buga kwallon ajin kwararru a shekarar 1997, ya kuma ba da muhimmiyar gudunmuwa a wasan tamaula a nahiyar Afirka da ma Turai.

Dan wasan ya ci kwallaye fiye da 350, sannan kuma ya ci wa kasarsa kwallaye 56 a wasanni 118.

Samuel Eto’o ya yi ritaya daga kulob din Qatar SC da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply