Home Kasashen Ketare EU ta amincewa kasashe 15 su shiga Turai amma babu Nijeriya

EU ta amincewa kasashe 15 su shiga Turai amma babu Nijeriya

187
0

Majalisar kungiyar Tarayyar Turai EU ta bude iyakokin ta ga kasashe 15 ciki banda Nijeriya.

Bayanan da aka samu a shafin intanet na kungiyar, ya nuna cewa har yanzu Nijeriya bata cikin kasashen da aka yarjewa mutanen ta su shiga tarayyar Turan.

Kasashe 15 da suka samu amincewar EU sun hada da Algeria, Australia, Canada, Georgia, Japan, Montenegro, Morocco.

Sauran sune New Zealand, Rwanda, Serbia, South Korea, Thailand, Tunisia, Uruguay sai kuma China da ake sa ran tabbatarwa ta hanyar yarjejeniya.

Kungiyar ta kuma yi alkawarin sabunta sunayen kasashen a duk bayan makonni biyu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply