Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi FAAC: Gwamnatin tarayya, jihohi, ƙananan hukumomi sun samu ₦639.901bn

FAAC: Gwamnatin tarayya, jihohi, ƙananan hukumomi sun samu ₦639.901bn

294
0

Gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi sun raba Naira Biliyan 639 da miliyan 901 a matsayin kuɗaɗen shigar watan Satumba da aka samu.

Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar kuɗi da kasafi Hassan Dodo, da ya bayyana haka a wata sanarwa, ya ambato babban sakataren ma’aikatar Aliyu Ahmed na faɗin yadda rabon kuɗin ya kasance a ƙarshen taron kwamitin rabon arziƙin ƙasa na FAAC.

Ahmed ya ce gwamnatin tarayya ta samu ₦255.748bn, jihohi 185.645bn sai ƙananan hukumomi da suka samu ₦138.444bn.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply