Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi FAAC ya raba ₦651.18bn a matsayin kuɗin shigar Yuni

FAAC ya raba ₦651.18bn a matsayin kuɗin shigar Yuni

151
0

Kwamitin rabon arziƙin ƙasa FAAC, ya raba ₦651.18bn ga gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi a matsayin kuɗaɗen shigar watan Yunin 2020.

A cewar ofishin babban Akantan tarayya bayanin rabon kuɗin na cikin wata sanarwar bayan taro da kwamitin ya fitar bayan kammala taronsa na wata-wata.

Wata sanarwa da ta fito daga Daraktan yaɗa labaran ofishin, ta ce kuɗin shigar da aka samu a watan ya kai ₦524.526bn, sai kuɗin shigar da aka samu a ɓangaren harajin VAT ya kai ₦128.826bn yayin da kuɗin da aka samu ta hanyar ribar musayar kuɗaɗe ta kai ₦42.832bn

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply