Home Coronavirus Facebook ya cire saƙon Trump kan riga-kafin Covid-19

Facebook ya cire saƙon Trump kan riga-kafin Covid-19

122
0

A ranar Larabar nan Facebook ya cire wani saƙo da shugaban Amirka Donald Trump ya wallafa, inda kamfanin ya ce bayanin ya saɓawa dokokinsu na yaɗa bayanan ƙarya kan coronavirus.

Saƙon na Trump dai ya ƙunshi wani bidiyon wata hira da abokai da aka yi a ranar, inda Trump ke iƙirarin cewa da alamu yara na ɗauke da riga-kafin Covid-19.

Mai magana da yawun Facebook ya ce bidiyon yana ɗauke da bayanan da ke cewa wani ɓangare na mutane na ɗauke da riga-kafin Covid-19 wanda haka kuma ya saɓa wa dokokin Facebook.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply