Home Kasashen Ketare Facebook ya tsawaita dakatarwar da ya yi wa Trump

Facebook ya tsawaita dakatarwar da ya yi wa Trump

193
0

Facebook ya dakatar da shugaba Donald Trump na Amirka daga yin amfani da dandalinsa, na tsawon akalla mako biyu.

shugaban kamfanin Mark Zugkerberg wanda ya bayyana haka a shafinsa, ya ce daukar wannan mataki ya zama wajibi ganin yadda shugaban ke kokarin fitar da kalaman tunzura jama’ar kasar.

Dakatarwar wadda aka fara sanya wa, ta kwana guda a ranar Laraba, an tsawaita ta ne saboda rashin dakatawar Trump daga yin kalaman tunzura jama’ar.

Zuckerberg ya ce an tsawaita dakatarwar ne saboda Trump na amfani da dandalinsu wajen tunzura mutane su tada zaune tsaye a don nuna adawa da gwamnatin da jama’a suka zaba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply