Home Farashin Kayan Abinci Buhun albasa daya ya kai Naira 80,000 a Sokoto

Buhun albasa daya ya kai Naira 80,000 a Sokoto

235
0

Farashin buhun tsohuwar albasa ya yi tashin gwauron-zabi a jihar Sokoto inda ake sayar da shi Naira 80,000, a dai-dai lokacin da ake sayar da buhun sabuwar albasar Naira 50,000.

DCL Hausa ta yi la’akarin cewa farashin albasar dai, ya yi wannan tsadar ne bisa dalilai irin su cutar corona, zanga-zangar EndSARS, da kuma ambaliyar ruwa da ta wanke gonakin albasar.

Yanzu dai al’umma na ci gaba da kokawa kan wannan tsada da ba a taba ganin ta ba tsawon lokaci.

Jihar Sakkwato dai ita ce jiha mafi girma da ake noman albasa a tarayyar Nijeriya da kuma ba ta taba fuskantar tsadar albasa ba a tarihin jihar sai a wannan karo.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply