Sabon Farin Wake ya shigo kasuwar Giwa ta jihar Kaduna inda ake sayar da buhunsa mai tiya 40 (nauyin kilo 100) a kan kudi Naira 13,500. A kasuwar Gurin, Fufore Adamawa da Dandume jihar Katsinan Nijeriya su ma a can Naira 13,500 ake sayar da buhun Farin Waken. Sai dai a jihar Gombe Naira 11,000 ake sayar da buhunsa.
Duba farashin sauran amfanin gonar da ma’aikatan DCL Hausa suka tattaro a wasu kasuwanni a jihohin Nijeriya. Latsa DOWNLOAD NOW a kasa don karanta cikakken farashin a tsarin PDF.
