DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeKasuwanciFarashin kayan abinci a Augustan 2026, mako na 35

Farashin kayan abinci a Augustan 2026, mako na 35

Binciken DCL Hausa kan farashin kayan abinci a wasu manyan kasuwannin Nijeriya ya nuna cewa an fara samun saukar farashi a wasu kayayyaki a wannan mako.

Shigowar sabon wake kasuwanni na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen rage farashin tsohon wake a wasu wurare.

SHINKAFAR HAUSA

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Saminaka (Kaduna) ₦120,000 ₦95,000 -₦25,000
Dawanau (Kano) ₦120,000 ₦120,000 —
Zamani (Adamawa) ₦110,000 ₦110,000 —
Giwa (Kaduna) ₦110,000 – ₦120,000 ₦110,000 – ₦120,000 —
Mai’adua (Katsina) ₦108,000 – ₦110,000 ₦110,000 Har zuwa +₦2,000
Mile 12 (Legas) ₦110,000 ₦110,000 —

SHINKAFA TA WAJE

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Giwa (Kaduna) ₦75,000 ₦75,000 —
Yola (Adamawa) — ₦75,000 – ₦80,000 —
Kano ₦60,000 ₦60,000 —
Mile 12 (Legas) ₦60,000 ₦60,000 —

WAKE

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Saminaka (Kaduna) ₦100,000 – ₦110,000 ₦100,000 – ₦110,000 —
Zamani (Adamawa) ₦100,000 – ₦110,000 ₦100,000 – ₦110,000 —
Giwa (Kaduna) ₦95,000 – ₦105,000 ₦90,000 – ₦95,000 Har zuwa -₦10,000
Mai’adua (Katsina) ₦60,000 – ₦65,000 ₦56,000 – ₦57,000 -₦4,000 zuwa -₦8,000
Dawanau (Kano) ₦80,000 – ₦90,000 Sabon: ₦65,000 / Tsoho: ₦75,000 Har zuwa -₦25,000
Mile 12 (Legas) ₦115,000 ₦155,000 +₦40,000

MASARA

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Mile 12 (Legas) ₦42,000 ₦40,000 -₦2,000
Adamawa ₦40,000 ₦40,000 —
Giwa (Kaduna) — ₦34,000 – ₦35,000 —
Mai’adua (Katsina) ₦37,000 ₦38,000 – ₦39,000 +₦1,000 zuwa +₦2,000
Saminaka (Kaduna) ₦28,000 ₦32,000 +₦4,000
Dawanau (Kano) ₦32,000 – ₦35,000 ₦36,000 Har zuwa +₦4,000

TALIYA (SPAGHETTI)

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Adamawa ₦13,000 – ₦13,500 ₦13,000 – ₦13,500 —
Dawanau (Kano) ₦13,000 – ₦13,500 ₦13,000 – ₦13,500 —
Giwa (Kaduna) ₦12,000 ₦12,000 —
Saminaka (Kaduna) ₦12,500 ₦12,500 —
Mai’adua (Katsina) ₦15,000 ₦15,000 —
Mile 12 (Legas) ₦16,000 ₦16,000 —

Abubuwan lura a wannan mako

  • Shinkafar Hausa ta samu mafi girman ragi a Saminaka, Kaduna, inda ta sauka da ₦25,000, daga ₦120,000 zuwa ₦95,000.
  • Wake ya samu gagarumin sauƙi a wasu kasuwanni sakamakon shigowar sabon wake.
  • Sai dai a Mile 12, Legas, wake ya yi tashin gwauron zabi, inda ya ƙaru da ₦40,000, daga ₦115,000 zuwa ₦155,000.
  • Masara ta sauka da ₦2,000 a Mile 12, amma ta ƙaru a Saminaka, Mai’adua da Dawanau.
  • Shinkafar waje da taliya sun kasance cikin yanayin kwanciyar hankali a mafi yawan kasuwannin da aka duba.
  • Duk da saukar farashi a wasu wurare, bayanan sun nuna cewa farashin kayan abinci ba ya tafiya a hanya guda a dukkan kasuwanni, musamman tsakanin kasuwannin Arewa da Mile 12 ta Legas.
Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata