DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeKasuwanciFarashin kayan abinci a Yulin 2026, mako na 29

Farashin kayan abinci a Yulin 2026, mako na 29

Binciken DCL Hausa kan farashin kayan abinci a wasu manyan kasuwannin Nijeriya ya nuna cewa an samu sauye-sauye a wannan mako. Yayin da farashin wasu kayan ya sauka a wasu kasuwanni, wasu kuma sun ƙaru ko suka ci gaba da kasancewa yadda suke, a daidai lokacin da manoma ke ci gaba da kokawa kan tsadar taki.

🟡 MASARA

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Saminaka (Kaduna) ₦26,000 ₦25,000 🟢 -₦1,000
Giwa (Kaduna) ₦32,000 ₦31,000 – ₦32,000 🟢 Saukar farashi
Dawanau (Kano) ₦32,000 – ₦35,000 ₦32,000 – ₦35,000 —
Zamani (Adamawa) ₦40,000 ₦38,000 🟢 -₦2,000
Mai’adua (Katsina) ₦37,000 ₦37,000 —

🟡 SHINKAFAR HAUSA (Jamila)

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Dawanau (Kano) ₦120,000 ₦120,000 —
Giwa (Kaduna) ₦115,000 ₦120,000 🔴 +₦5,000
Zamani (Adamawa) ₦102,000 ₦105,000 🔴 +₦3,000
Mai’adua (Katsina) ₦100,000 ₦105,000 🔴 +₦5,000
Saminaka (Kaduna) ₦100,000 ₦100,000 —

🟡 SHINKAFA TA WAJE (Foreign Rice)

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Giwa (Kaduna) ₦75,000 ₦80,000 🔴 +₦5,000
Zamani (Adamawa) ₦70,000 ₦70,000 – ₦75,000 🔴 Har zuwa +₦5,000
Dawanau (Kano) ₦60,000 ₦58,000 – ₦60,000 🟢 Har zuwa -₦2,000

🟡 WAKE

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Giwa (Kaduna) ₦95,000 – ₦105,000 ₦100,000 – ₦110,000 🔴 +₦5,000
Dawanau (Kano) ₦95,000 – ₦100,000 ₦110,000 🔴 +₦10,000 zuwa ₦15,000
Saminaka (Kaduna) ₦100,000 ₦95,000 🟢 -₦5,000
Zamani (Adamawa) ₦90,000 – ₦95,000 ₦95,000 – ₦100,000 🔴 +₦5,000
Mai’adua (Katsina) Ƙarami: ₦100,000Babba: ₦110,000 Ƙarami: ₦100,000Babba: ₦110,000 —

🟡 TALIYA (Spaghetti)

Kasuwa Mako na baya Mako na yanzu Bambanci
Giwa (Kaduna) ₦12,000 ₦12,000 —
Saminaka (Kaduna) ₦12,500 ₦12,500 —
Zamani (Adamawa) ₦13,500 ₦13,500 —
Dawanau (Kano) ₦13,500 ₦13,500 —
Mai’adua (Katsina) ₦14,000 ₦14,000 —

Abubuwan lura a wannan mako

  • Masara ta sauka a Saminaka (Kaduna) da Zamani (Adamawa), yayin da farashinta bai canza ba a Dawanau (Kano) da Mai’adua (Katsina).
  • Shinkafar Hausa (Jamila) ta ƙaru a Giwa (Kaduna), Mai’adua (Katsina) da Zamani (Adamawa), amma ta ci gaba da kasancewa ₦120,000 a Dawanau (Kano).
  • Shinkafa ta waje ta ƙara tsada a Giwa (Kaduna) da Zamani (Adamawa), yayin da aka samu ɗan ragi a Dawanau (Kano).
  • Wake ya fi samun ƙarin farashi a Dawanau (Kano), inda ya haura zuwa ₦110,000, yayin da aka samu ragin ₦5,000 a Saminaka (Kaduna).
  • Taliya ta ci gaba da kasancewa daidai a dukkan kasuwannin da DCL Hausa ya bibbiya, ba tare da wani canjin farashi ba.
  • Duk da an samu saukar farashin wasu kayan, musamman masara, ana ci gaba da samun ƙarin farashi a shinkafa da wake a wasu kasuwanni, lamarin da ke nuna cewa kasuwar kayan abinci ba ta daidaita gaba ɗaya ba.
  • Wannan sauyin na faruwa ne a daidai lokacin da manoma ke ci gaba da nuna damuwa kan tsadar taki, wanda zai iya yin tasiri ga farashin amfanin gona a watanni masu zuwa.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata