Manoma na cigaba da darawa ganin yadda farashin masara ke ta kara inganta a kasuwanni. A wannan makon buhun masarar mai cin tiya 40 ya kama N19,500 a Damagaram Jamhuriyar Nijar, N19,000 a Giwa jihar Kaduna da Dandume jihar Katsina. Mile 12 International Market Lagos kuwa N21,000, Mai’adua jihar Katsina N20,500.
Karanta cikakken farashin kayan abincin na wannan makon a shafinmu.
Kasuwar Mai’adua jihar Katsina
Masara N20,500
Shinkafar Hausa N40,000
Shinkafar bature N20,000
Wake fari N30,000
Waken soya N29,000
Taliyar spaghetti N4,200
Gero N19,000
Kwantalora N17,600
———————————
Kasuwar Mile 12 International Market Lagos
Masara N21,000
Shinkafar bature N24,000
Wake Fari N28,000
Waken soya N26,000
Gero N22,000
Taliyar spaghetti N4,200
Kwantalora N17,500
——————————–
Kasuwar Dandume, jihar Katsina
Masara N19,000
Shinkafar Hausa N40,500
Shinkafar bature N26,000
Wake Fari N31,000
Waken soya N28,500
Gero N20,000
Taliyar spaghetti N4,200
Kwantalora N20,500
———————————–
Kasuwar Giwa, jihar Kaduna
Masara N19,000
Shinkafar Hausa N42,000
Shinkafar bature 27,500
Wake fari N28,000
Waken soya N27,000
Taliyar spaghetti N4,150
Gero N20,000
Kwantalora N21,000
———————————–
Kasuwar Damagaram, Jamhuriyar Nijar
Masara N19,500
Shinkafar bature N20,800
Wake fari N29,500
Waken soya N28,500
Taliyar spaghetti N4,700
Gero N22,500
Kwantalora N17,700
————————————
Kasuwar Dawanau, jihar Kano
Masara ₦19,000
Shinkafar bature ₦24,000
/ta Hausa ₦38,000
Taliyar Spaghetti ₦4,200
Taliyar Spaghetti yar waje ₦4,750
Wake Fari. ₦32,500
Waken Soya ₦28,000
Gero ₦19,500
Kwantalora ₦20,000
Mun samu wadannan bayanai daga wurin:
Alhaji Shehu Nayaya, dan kasuwa a kasuwar Dandume jihar Katsina Najeriya
2. Suleiman Hassan, dan kasuwa a Giwa jihar Kaduna
3. Abdullahi Malami Mohd Jos, kasuwar Mile 12 Lagos
4. Malam Yahya Isa, dan kasuwa a kasuwar Marche a Ndajamena Chadi
5. Salisu Ahmadu Daura, dan kasuwa a kasuwar Dawanau ta Kano
6. Yacouba Umaru Maigizawa, wakilin DCL Hausa a Damagaram Nijar.
