A ranar Juma’ar nan ne gwamnatin tarayya ta kafa kwamitocin farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya bayan Covid-19.
Da take ƙaddamar da kwamitocin a Abuja, Ministar kuɗi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmed, ta buƙaci wakilan kwamitocin su tabbatar abun da ya biyo bayan Covid-19 bai yi illa ga ƴan Nijeriya da tattalin arziƙin ƙasar ba.
Ahmed ta bayyana yadda cutar ta haifar da mummunar illa ga ƙananan ƴan kasuwa, magidanta da manoma a faɗin duniya.
Saidai ta ce gwamnatin tarayya a madadin jihohi, za ta ciwo bashin dala miliyan 750 don tallafa wa ƙananan ƴan kasuwa da magidanta gajiyayyu.
