Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Fasakwaurin shinkafar waje na barazanar durkusar da masu sarrafa shinkafa a Niejriya

Fasakwaurin shinkafar waje na barazanar durkusar da masu sarrafa shinkafa a Niejriya

35
0

Kungiyar masu sarrafa shinkafar gida ta koka wa gwamnatin Nijeriya game da masu fasa kwaurin shinkafar waje, cewa Nijeriya na gab da yin asarar akalla sama da Naira Tiriliyan uku da masu sarrafa shinkafar suka zuba a matsayin jari.

 

Daraktan kungiyar masu sana’anta shinkafar yar gida, RIPAN, Andy Ekwelem ne ya yi wannan korafin a karshen makon nan da suke zantawa ta manhajar whatsapp a Abuja., acewar jaridar DailyTrust.

RIPAN ta bukaci a haramta tu’ammuli da shinkafa yar waje tare da kulle duk masu fasa kwaurinta, dilolinta, tana mai bukatar a rinka kama masu fasa kwaurin shinkafar da laifin yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

 

DCL Hausa ta samu labarin cewa kungiyar ta RIPAN ta yi zargin cewa tun bayan da Nijeriya ta sake bude iyakokinta na tudu fasa kwaurin shinkafa ya kara kamari a iyakokin kasar da kasar Benin da kuma jamhuriyar Nijar ta yankin Daura.

 

Labarai Masu AlakaDA DUMI-DUMI: Buhari ya bude iyakokin Najeriya

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply