Shugabannin marasa rinjaye a majalisar Dattawan Nijeriya sun yi fatar cewa sabbin shugabannin tsaron da aka naɗa za su kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.
Da yake magana kan naɗin sabbin hafsoshin, shugaban marasa rinjayen Enyinnaya Abaribe, ya ce duk da majalisar ta daɗe tana kiran a sauya shugabannin tsaron, abun da ya faru jiya ya fi rashin yinsa.
Ya ce suna fatan wannan mataki zai ƙarfafa samar da tsaro a ƙasar.
