DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeKasuwanciFCCPC za ta binciki dalilin da ya sa buhun siminti ya kai...

FCCPC za ta binciki dalilin da ya sa buhun siminti ya kai N15,000 a Nijeriya

FCCPC za ta binciki dalilin da ya sa buhun siminti ya kai N15,000 a Nijeriya

Hukumar kare hakkin masu sayayya ta Nijeriya (FCCPC) ta fara zurfafa bincike kan yiwuwar samun magudi a farashi ko wasu matakan da suka saba wa dokar gasa a kasuwar siminti ta Nijeriya, yayin da farashin buhun siminti mai nauyin kilogram 50 ya kai tsakanin N13,000 zuwa N15,000 a wasu sassan ƙasar.

Jaridar The Guardian ta ruwaito binciken, wanda sashen yaki da hanyoyin kasuwanci masu tauye gasa na hukumar ya gudanar na tsawon watanni uku, ya biyo bayan yawaitar korafe-korafen da jama’a ke yi kan hauhawar farashin siminti.

A cewar rahoton binciken farko mai shafuka 40, Nijeriya na da ƙarfin samar da siminti da aka kiyasta tsakanin tan miliyan 60 zuwa 65 a shekara, yayin da bukatar cikin gida take kusan tan miliyan 25 zuwa 30 kawai.

Hukumar ta ce wannan na nufin akwai gagarumin rarar ƙarfin samar da siminti, kuma bisa tsarin kasuwa mai gasa, irin wannan yanayi ya kamata ya taimaka wajen rage farashin, ba ƙara shi ba.

FCCPC ta bayyana cewa buhun siminti mai nauyin kilo 50 wanda ake sayarwa tsakanin N9,300 zuwa N9,700 a watan Janairun 2026, ya tashi zuwa tsakanin N10,500 da N13,000 a tsakiyar shekara. Zuwa watan Yuli kuma, an samu rahotannin farashin da ya kai N13,000 zuwa N15,000 a wasu wurare.

Hukumar ta kuma kwatanta kasuwar siminti ta Nijeriya da ta Kenya, Tanzania, Afirka ta Kudu, Masar, Morocco, Aljeriya da Togo, inda ta yi la’akari da abubuwa kamar yawan jama’a, samar da siminti, bukatar cikin gida da farashin dillalai.

Misalin da FCCPC ta buga na farashin buhun siminti mai nauyin kilo 50 a Kenya yana kusan dala 5.40, wanda yake daidai da kusan N7,344, yayin da a Tanzania yake kusan dala 4.80, wato N6,528. A Togo kuwa, inda hukumar ta ce babu ma’adinan limestone, farashin yana kusan dala 6.75, wato N9,180.

Saboda haka, hukumar ta ce tana son tabbatar da ko dalilan da kamfanonin siminti ke bayarwa kan hauhawar farashin sun isa su bayyana girman tashin farashin da aka gani a Nijeriya.

Masu ruwa da tsaki a masana’antar sun danganta hauhawar farashin da tsadar makamashi, faduwar darajar naira da tasirinta kan kayan aikin da ake shigowa da su daga ketare, da kuma karin kudin sufuri da jigilar kayayyaki.

Sai dai FCCPC ta ce tana tantance wadannan bayanai ta hanyar duba ainihin kudin samarwa, yadda ake amfani da karfin masana’antu, farashin kayayyaki da sauran yanayin kasuwa.

Tuni dai hukumar ta ce ta riga ta aika da sanarwar fara bincike da sammacin neman bayanai ga wasu manyan masu ruwa da tsaki a masana’antar.

Inda ake bukatar kamfanonin su gabatar da bayanai kan yadda suke tsara farashinsu, yawan abin da suke samarwa, yadda suke amfani da karfin masana’antunsu, fitar da siminti zuwa kasashen waje da kuma abokan hulɗar kasuwancinsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata