Home Labarai FFK: Ba mu buƙatar irinka a APC – Martanin Bashir Ahmad

FFK: Ba mu buƙatar irinka a APC – Martanin Bashir Ahmad

37
0

Wani daga cikin masu ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara, Bashir Ahmad ya yi martani ga labarin sauya shekar Femi Fani Kayode daga PDP zuwa jam’iyyar APC.

A shekarar 2019 ne dai Fani-Kayode ya bar APC zuwa PDP, yana mai cewa bayyana jam’iyyar a matsayin kwale-kwalen da ke kokarin nutse wa cikin ruwa.

Saidai Bashir Ahmad ya ce idan da shi ne Fani-Kayode, ba zai taba tunanin komawa jam’iyyar da ya bayyana ta Almajirai ba.

A cikin jerin sakonnin twitter da ya wallafa, Ahmad ya ce “yanzu yaji labarin Fani-Kayode na kokarin shiga jam’iyyar ‘yan Boko Haram, tare da fatan dai ya samu horo sosai domin zama kwamanda.

Ahmad yana yi wa Fani-Kayode martani a wani sakon Twitter da ya taba wallafa wa a shekarar 2014, yana mai cewa jam’iyyar APC wani bangare ne na siyasar Boko Haram, yayinda Boko Haram kuma ita ce rundunar yakin APC.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply