Home Labarai FG ta amince da ƙarin asibitoci 12 su riƙa gashin kansa

FG ta amince da ƙarin asibitoci 12 su riƙa gashin kansa

27
0

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya amince da Karin asibitoci 12 da za su rika yin gashin kansa, karkashin shirin hadin guiwar kula da lafiyar masu fama da cutar da aka bullo da shi don rage masu sama da kashi 50 na kudin da suke kashe wa.

Ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja kan bikin ranar kansa ta duniya da aka gudanar a ranar Alhamis, domin kara wayae da kan jama’a kan cutar da yadda za a dauki matakan kariya da yadda ake saurin gane an kamu da ita.

Ya ce yanzu haka ma’aiaktar Lafiya ta Tarayya karkashin kulawarsa, na koarin inganta hanyoyin kula da masu cutar musamman bangaren gwaje-gwaje da gashi ta hanyar samar da injinan gashin a asibitocin koyarwa na jami’o’in Enugu, Benin, Sokoto Ibadan da ABU Zaria.

Ehanire ya ce Karin asibitocin na daga cikin matsayar da suka cimmawa daga bikin ranar cutar na bara, na kara yawan asibitocin daga bakwai zuwa 18 a halin yanzu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply