Home Coronavirus FG ta bukaci jihohi su hana bukukuwan sallah

FG ta bukaci jihohi su hana bukukuwan sallah

143
0

Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha yace gwamnatin tarayya ta ji dadin yadda wasu gwamnatocin jihohi suka soke bukukuwan babbar sallah mai zuwa.

Boss Mustapha, wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da corona na Nijeriya yace, gwamnatin tarayya na fatar sauran jihohi ma su hana.

Jihohin Kano da Jigawa dai tuni suka sanar da soke dukkanin shagulgulan sallah.

Gwamnatin Nijeriya ta bukaci mutane su ci gaba da bin dokokin da aka gindaya don hana yadawa ko kamuwa da cutar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply