Home Labarai FG ta yi wa ƴan gidan yari 4,000 afuwa

FG ta yi wa ƴan gidan yari 4,000 afuwa

39
0

Ministan cikin gidan Rauf Aregbesola, ya ce gwamnatin tarayya ta yi afuwa ga ‘yan gidan yari sama da 4,000 a karkashin shirin afuwa na gwamnatin tarayya da aka fara a shekarar 2020, domin rage cinkoso a gidajen yari.

Ministan ya yi korafin cewa gidajen yarin kasar na fuskantar kalubalen yawaitar mutanen da ke zaman jiran shari’a da suke neman zarta wadanda aka yi wa hukunci.

Ya ce wannan ba karamin koma baya bane ga kokarin da ake na kula da ‘yan gidan yarin, wanda hakan ke janyo matsalolin da ake fuskanta na fasa gidajen yari da yiwuwar guduwar wadanda ake tsare da su wanda ya sanya jami’an hukumar ke matukar shan wahala wajen tsarewa da kuma kashe kudi.

Da yake magana a wajen taron babban kwantirolan hukumar kula da gidajen yarin kasar Ja’afaru Ahmed wanda ya ce wannan shi ne karo na biyar da ake kaddamar da motocin tun bayan hawansa shugabancin hukumar, ya ce daukar masu laifi zuwa kotu na daya daga cikin kalubalen da suke fuskanta da yake kara janyo cinkoso a gidajen yarin.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply