Home Labarai FG za ta dakatar da albashin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya

FG za ta dakatar da albashin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya

29
0

Gwamnatin tarayya ta yi barazanar dakatar da albashin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya da ke yajin aikin sai baba ta gani.

Ministan kwadago Sanata Chris Ngige ya bayyana cewa sashe na 43 na dokar kasuwanci ta 2004, da dokar kwadago ta duniya ta ba gwamnati damar dakatar da albashin ma’aikata a lokacin da suke yajin aiki.

Ya yi gargadin cewa gwamnati za ta yi amfani da wannan dokar idan har kungiyoyin ma’aiatan ba su bi tsarin da doka ta tanadar na tattaunawar sasanci ba.

Ngige, ya ce ba daidai ba ne kungiyoyin su shiga yajin aikin a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin magance masu matsalolinsu, kamar sashe na 7 da na 8 na dokar kwadagon ya tanadar.

Ministan ya ce yajin aikin da kungiyoyin SSANU da NASU ke yi ya saba wa dokokin kwadagon Nijeriya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply