Home Sabon Labari FIFA: an dakatar da Samson Siasia har abada daga shiga shirgin wasannin...

FIFA: an dakatar da Samson Siasia har abada daga shiga shirgin wasannin kwallon kafa

67
0

Daga Ahmadu Rabe

Hukumar kwallon kafa ta duniya -FIFA- ta dakatar da tsohon kocin tawagar Nijeriya ta Super Eagles Mr. Samson Siasia daga shiga harkokin wasan kwallon kafa.

Hukumar -FIFA- ta tabbatar wa manema labarai cewa an dakatar da shi ne dakatarwa ta har abada sakamakon samunsa da badakalar sayar da wasa lokacin yana horaswa.

Siasia ya zamo kocin Nigeria daga shekarar 2010 zuwa 2011, sannan ya kara samun damar horas da kungiyar ta Super Eagles na dan wani lokaci a shekarar 2016.

Ya zuwa yanzu dai Siasia mai shekaru 52 bai ce uffan ba kan dakatarwar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply