Hukumar kula da wasan ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) ta amince da shirin gwamnatin Nijeriya na sake fasalin harkokin gudanar da wasan ƙwallon ƙafa a ƙasar, biyo bayan murabus ɗin da shugabanni da babban sakataren hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) suka yi gaba ɗaya.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa shugaban hukumar wasanni ta ƙasa (NSC), Shehu Dikko, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wata tattaunawa da gidan talabijin na ARISE NEWS, bayan ganawarsa da jami’an FIFA da hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) a ƙasar Switzerland.
Dikko ya bayyana cewa gwamnati ta miƙa shawarwarin sauye-sauyen ne ga FIFA domin cike giɓin shugabanci da murabus ɗin ya haifar, duba da cewa kundin dokokin NFF ba shi da tanadin yadda za a tafiyar da hukumar idan dukkan mambobin suka sauka a lokaci ɗaya.
A cewar Dikko, FIFA ta amince da murabus ɗin shugabannin tare da goyon bayan aiwatar da garambawul ga tsarin ƙwallon ƙafa a Nijeriya, matuƙar aka bi ƙa’idojin da suka dace.
Saukar shugabannin NFF, ciki har da shugaban hukumar Ibrahim Gusau da babban sakatare Mohammed Sanusi a ranar 27 ga Agusta, ta biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da suka biyo bayan gazawar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na ƙasa, musamman Super Eagles da Super Falcons, wajen samun gurbin zuwa gasar cin kofin duniya.
Dikko ya bayyana cewa FIFA na iya kafa kwamitin sasanta al’amura na musamman (Normalisation Committee) mai zaman kansa wanda zai jagoranci aikin sauye-sauyen na tsawon watanni shida zuwa shekara guda. Ya ce membobin kwamitin ba za su fito daga cikin masu ruwa da tsaki da ke da sha’awar yin takara a zaɓe mai zuwa ba, domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Babban jigon sauye-sauyen zai shafi fasalin zaɓen NFF, inda gwamnati ke duba yiwuwar sauya tsarin ta yadda duk wani ɗan takarar shugabanci zai fito da cikakkiyar tawagarsa—da suka haɗa da mataimakinsa, sakatare, da masu tallata hukumar—kafin zaɓe domin masu kaɗa ƙuri’a su zaɓi tawaga mai manufa ɗaya.
Dikko ya ƙara da cewa an riga an fara tattaunawa da mambobin majalisar NFF kan daftarin sauye-sauyen, kafin tawagar FIFA ta kawo ziyara Nijeriya domin kammala shirye-shiryen.
