Ministan sufurin saman Nijeriya Sanata Hadi Sirika ya ce tuni filayen jiragen Abuja, Lagos da Kano suka gama shirye-shiryen fara jigilar fasinja a cikin ƙasar.
Ministan wanda ya bayyana haka a Abuja, ya ce filayen jiragen uku za su fara aiki a gobe Laraba.
Ministan ya yi kira ga fasinjoji da ma’aikata da su yi biyayya ga ƙa’idojin da aka gindaya a filayen jiragen.
