Home Kasashen Ketare Firimiya: Aston Villa da lallasa Liverpool da ci 7-2

Firimiya: Aston Villa da lallasa Liverpool da ci 7-2

110
0

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool mai rike da kofin firimiyar Ingila ta yi rashin nasara a gidan kungiyar Aston Villa inda aka zura mata kwallaye 7-2.

Dan wasan gaban Aston Villa Ollie Watkins ya samu nasarar jefa kwallaye 3 rigis a wasan inda ya sharara kwallo a ragar Liverpool a mintuna 4′- 22′-da kuma 39′.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci Aston Villa din suka kara yin ta maza, inda suka kara kwallaye 3 a ragar bakin.

Mohammed Salah ne ya ci wa Liverpool din kwallaye 2 da ta ci a wasan.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply