Daga Zaharaddeen Umar
Kulob din Manchester United na Ingila ya kammala cinikin Harry Maguire kan kudi Euro milyan 85
Harry Maguire ya yi suna a kulob dinsa na Leicester kuma ya kware a wurin tsare baya a wurin taka leda.
An dauki dogon lokaci kafin United ta yi nasarar sayen dan wasan mai shekaru 26. Da farko United ta yi tayin da bai faranta wa mahukuntan kulob din Leicester ba. Amma daga karshe sun yi ta maza sun yarda za su biya Euro Milyan 85 kamar yadda Leicester ta bukata tun da farko.

Dan wasa Maguire dai yanzu ya shiga sahun ‘yan wasa masu tsada a duniya. Koda yake akwai wagegen gibi a tsakaninsa da Neymar wanda kafin ya baro kungiyar Barcelona sai da kulob dinsa na yanzu, PSG na Faransa, ya biya wajen Euro Milyan 220.
